Game da Mu

A wannan shafi zamu gabatar maku da manufofinmu, burikan mu, da tarihin mu. Sannan zamu gabatar muku da wadanda suka assasa  wannan cibiya mai albarka.

Sakon mu Gareku

Imam Sufyan Assauri ya bada labarin lokacin da ya fara shiga aji daukan darasi, Mahaifiyar sa ta ce dashi “Idan har ka rubuta kalmomi goma imaninka bai karu ba to ka tuntubi kanka”.

Hangenmu

Samar da ilimi da ya game duk babukan da musulmi ya kamata ya sani dan kyautata addininsa saboda rabauta rana gobe Qiyama. Mu tuna "Neman ilimi wajibi ne akan kowane musulmi”

Tarihinmu

Khairu Ummah an assasata a shekarar 2015 a matsayin hanyar koyar da al’umar musulmai da tunatar dasu ta hanyar amfani da Fasahar sadarwa. A farko an fara amfani da filin sada zumunta na Facebook dan yada wannan manufa. Daga bisani aka yi tunanin kara fadada abin ta hanyar samar da wata makaranta a yanar gizogizo da za ta zamo wata cibiya dan kara kusantar da ilimi ga al’umma cikin sauki. Bayan wannan tunani, a shekarar 2017 wanda ya Kafa wannan makaranta watau Abubakar Sani Ali yaje ya tuntubi Malaminsa watau Mal Abdallah Usman. Malam ya bashi goyon bayan assasasa wannan makaranta mai albarka tare da bashi duk wani taimako wanda zai iya na ganin wannan makaranta ta zamanto abar buga misali. Daga nan ne fa ya fara aiki dan ganin wannan makaranta ta kafu. A shekara ta 2018 aka yada wannan shafi na yanar gizo akan internet inda duk jama’a za su iya shiga dan amfana da kuma more romon ilimi daga bakin manyan malamai.

Burukanmu

  1. Koyar da al’ummar musulmi ingantancen addini wanda yake dogara da Alqur’ani da Sunna a zamanance, cikin sauki ta hanyar yanar gizo gizo.
  2. Samar wa al’umma hanya mai saukin isuwa gareta dan koyon addini suna zaune a gidajensu.
  3. Yada ilimin addinin musulunci a kyauta ga daliban ilimi
  4. Jajircewa wurin samar da malamai masani kowane fanni dan samar da ingantaccan ilimi.

Hadu da mu

Founder

Abubakar Sani Ali

I am text block. Click edit button to change this text. Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. 

Co-founder

Abdulhakeem Bashir

I am text block. Click edit button to change this text. Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. 

co-founder

Abba Suraj Salihu

I am text block. Click edit button to change this text. Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. 

co-founder

Sulaiman Abdulqadir

I am text block. Click edit button to change this text. Lorem ipsum dolor sit amet, consectetur adipiscing elit. 

Scroll to Top